Search
Close this search box.

Iran Tace: Aikin Hadin Giwa Tsakaninta Da Rasha Babban Mataki Ne Na Karya Takunkuman Tattalin Arzikin Da Kasashen Yamma Suka Dorawa Kasashen Biyu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa idan an aiwatar da aikin hadin giwa tsakanin Iran da Rasha wannan zai zama babbar nasara ga

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa idan an aiwatar da aikin hadin giwa tsakanin Iran da Rasha wannan zai zama babbar nasara ga kasashen biyu wajen karya tasirin takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dorawa kasashen biyu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin da ya ke ganawa da shugaban gwamnati ko firai ministan kasar Rasha Mikhail Mishustin wanda yake ziyarara aiki a nan Tehran tun jiya Litinin.

Labarin ya kara da cewa Mishustin ya isa birnin Tehran ne a jiya Litinin tare da tawagar yan kasuwa da manya manyan jami’an gwamnatin kasar Rasha da kuma shuwagabannin kamfanoni daban daban na kasar Rasha.

Shugaba Pezeskiyan ya kara da cewa, aikin hadin giwa mafi  muhimmanci wanda kasashen biyu zasu sa a gaba shi ne maida Iran hanyar wucewa da  iskar gas na kasar Rasha zuwa kasashen Asia.

Har’ila yau akwai wasu ayyukan hadin giwa tsakanin Iran da Rasha a kungiyoyin BRICS da kuma SCO ko kuma ‘Shanghai Cooperation Organization’. Wadannan ayyukan idan sun kankama tasirin takunkuman tattalin arzikin kasashen yamma a kan kasashen biyu zai ragu sosai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments