Iran Ta Yo Tir Da Hare Haren Da HKI Ta Kai Kan Asbitin Wucin Gadin Na Iraniyawa a Kan Iyakar Kasashen Lebanon Da Siriya

Iran ta yi allawadai da hare haren da HKI ta kai kan asbitin wucin gadi na kasar wanda ta kafa a kan iyakar kasashen Lebanon

Iran ta yi allawadai da hare haren da HKI ta kai kan asbitin wucin gadi na kasar wanda ta kafa a kan iyakar kasashen Lebanon da Siriya don tallafawa mutanen kasar Lebanon wadanda suke shigowa kasar Siriya saboda tsira da ransu daga hare hare sojojin HKI a kan kasarsu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa dukkan kayakin asbitin da suke cikin asbitin sun kone sai dai babu labarin wani ya ransa ransa ko ya ji ciwa sanadiyyar hare hare.,

Mai magana da yawon ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghae ya ce hare haren sun tabbatar da cewa HKI bata mutunta dokokin kasa da kasa dangane da yan gudun hijira da kuma masu bukatar kayakin  agaji.

Daga ciki har da dokokin kasa da kasa wadanda suka shafi babbar kungiyar Red Cross ko Hilar Ahmar ta duniya.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne sojojin HKI suka fara kai hare haren a kan kasashen Falasdinu da Lebanon da nufin kwato yahudawan da kungiyar Hamas ta tsare a gaza, da kuma shafe kungiyar daga doron kasa. Amma fiye da shekara guda Kenan ake fafatawa da Falasdinawan ba tare da samun nasara ko da guda daga cikin bukatunta ba.

Sannan sojojin yahudawan sun yi kokarin shiga kasar Lebanon ta kasa tun fiye da makonni 3 da suka gabata amma dakarun  kungiyar Hizbullah sun hanasu yin hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments