Iran Ta Yi Tir Da Kallaman Ministan Isra’ila Na Neman A Karbe Yammacin Gabar Kogin Jordan

Iran ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan kiran da wani ministan Isra’ila ya yi na neman a karbe yankin yammacin gabar kogin Jordan

Iran ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan kiran da wani ministan Isra’ila ya yi na neman a karbe yankin yammacin gabar kogin Jordan da isra’ila ta mamaye.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baghaei ya fada a ranar Laraba cewa, wannan wata alama ce ta “dabi’ar wariyar launin fata.

Baghaei ya yi Allah wadai ne a cikin wata rubutacciyar sanarwa, yana mai nuni da kalaman ministan kudi na Isra’ila Bezalel Smotrich a ranar 11 ga watan Nuwamba.  

Shi dai ministan na Isra’ila ya ce ya bayar da umarnin shirye-shiryen karbe yankin yammacin kogin Jordan ne tare da fatan gwamnatin kasar za ta samu ikon mallakar yankin a shekarar 2025. 

Kakakin ma’aikatar harekokin wajen kasar ta Iran ya yi kira da a dauki kwakkwaran matakai na kasa da kasa da kwamitin sulhu na MDD domin kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Falastinu da kuma yakin da gwamnatin kasar ke yi a Lebanon da kuma yammacin Asiya.

Ya ce irin wannan yunkurin na kisan kare dangi ba zai taba yin cikas ga muradin al’ummar Falasdinu da kuma kudurinsu na ‘yantar da yankunansu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments