Iran, Ta Kirayi Wakilan Kasashen Turai Kan Zarginta Da Tura Makamai Masu Linzami

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kirayi wakilan kasashen Birtaniya, Faransa, Jamus, da Netherlands don nuna rashin amincewarta da “kalamai marasa tushe daga wadannan kasashen na

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kirayi wakilan kasashen Birtaniya, Faransa, Jamus, da Netherlands don nuna rashin amincewarta da “kalamai marasa tushe daga wadannan kasashen na zarginta da tura makamai masu linzami.

Takaddamar dai ta samo asali ne daga zarge-zargen da ake yi na cewa Iran ta mika wa Rasha makamai masu linzami da za ta yi amfani da su a yakin Ukraine, wanda Tehran ta musanta.

An gayyaci jami’an diflomasiyyar yau Alhamis, biyo bayan ikirarin da gwamnatocin kasashensu suka yi na mikawa kasar Rasha makamai masu linzami da kuma takunkumin da suka sanar sun kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Darakta Janar na Ma’aikatar Harkokin wajen Iran na sashen Yammacin Turai, Majid Nili, ya gabatar da kakkausar suka ta Iran ga kasashen.

Mista Nili, ya soki kalaman gwamnatocin kasashen Turan,  wadanda ya danganta da nuna kiyaya kan al’ummar Iran, yana kuma mai gargadin cewa Iran za ta mayar da martanin da ya dace, idan har kasashen suka dawwama akan zargin.

Iran, wacce a hukumance ke bayar da shawarwarin warware yakin Ukraine cikin lumana, ta sha musanta tuwa makamai masu linzami zuwa Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments