Iran ta jinjinawa Sin da Rasha a matsayin kawayenta na kut-da-kut

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jinjinawa kasashen Sin da Rasha a matsayin abokan hulda na kut-da-kut da kasar, yayin da ya isa birnin Beijing

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jinjinawa kasashen Sin da Rasha a matsayin abokan hulda na kut-da-kut da kasar, yayin da ya isa birnin Beijing domin yin shawarwari da manyan jami’an kasar Sin, gabanin yin tattaunawa zagaye ta uku da Amurka kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Abbas Araghchi ya shaida wa kafar yada labaran Iran a babban birnin kasar Sin a ranar Laraba cewa, “Sin da Rasha abokan hulda ne na kut da kut da suka tsaya tare da mu a lokutan wahala, don yana da kyau da ma’ana mu ci gaba da tuntubar juna tare da su a bangarori daban-daban, musamman ma yanzu da ake tattaunawa da Amurka.”

“Ya zama dole mu sanar da abokanmu a kasar Sin cikakken bayani game da al’amuran da ke gudana tare da tuntubarsu.” Inji shi.

Yayin da yake jaddada cewa, ya yi irin wannan ganawa da manyan jami’an kasar Rasha a birnin Moscow a makon jiya, Araghchi ya ce yana fatan samun kyakkyawar tattaunawa da mahukuntan Beijing, domin isar da sakon shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ga mahukuntan kasar Sin.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya ce, “A baya kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa kuma mai ma’ana a batun nukiliyar kasar Iran, kuma ko shakka ana bukatar hakan.

Za mu ci gaba da tuntubar Sin a matsayinta na mamba a kwamitin sulhun MDD, mamba a kwamitin gudanarwar hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, bugu da kari kawa  ta kut-da-kut ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inji ministan harkokin wajen kasar ta Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments