Iran Ta Jaddada Cewa Makaman Nukiliyar Haramtacciyar Kasar Isra’ila Barazana Ne Ga Yankin

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Makaman nukiliyar haramtacciyar kasar Isra’ila, babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Makaman nukiliyar haramtacciyar kasar Isra’ila, babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya baki daya

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya kuma wakilinta na din din din a Majalisar Amir Sa’id Irawani, ya jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila tana barazana ga sauran kasashen yankin ta hanyar yin amfani da makaman na nukiliya kansu, kuma rumbun makamanta na nukiliya yana  matsayin babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya baki daya.

A zaman taron Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata a daidai lokacin da ake gudanar da ranar yaki da gwaje-gwajen makaman nukiliya ta duniya: Amir Sa’id Irawani, ya kara da cewa: Tunawa da wannan rana, wata dama ce ga kasashen duniya da zasu yi amfani da ita wajen tilastawa haramtacciyar kasar Isra’ila shiga cikin yerjejeniyar hana kera makaman nukiliya tare da yaduwarsu a duniya, ba tare da wani sharadi ba, gami da sanya dukkan cibiyoyinta na nukiliya karkashin cikakkiyar kulawar hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya. Sakamakon yanzu ana cikin halin matukar damuwa, saboda haramtacciyar kasar Isra’ila tana barazana ga sauran kasashen yankin wajen murkushe su da makamanta na nukiliya, kuma ana daukar makamanta na nukiliyar a matsayin babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments