Iran ta jaddada cewa: Ba Zata Taba Amincewa Da Gudanar Da Tattaunawa Kan Tsaronta Ba

Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Iran ba za ta taba gudanar da shawarwari kan tsaronta ba A cikin jawabinsa na shirye-shiryen shirin zaman

Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Iran ba za ta taba gudanar da shawarwari kan tsaronta ba

A cikin jawabinsa na shirye-shiryen shirin zaman taron Carnegie kan manufofin nukiliya na kasa da kasa da aka soke a yanzu, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa kamfanonin Amurka za su iya cin gajiyar damar dala tiriliyan da tattalin arzikin Iran ke samarwa kuma kasuwar Iran za ta iya farfado da masana’antar nukiliyar Amurka da ta tsaya cak.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba ta da niyyar yin shawarwari da tattaunawa a fili a bainar jama’a.”

Araqchi ya ci gaba da cewa, “A cikin jawabinsa, ya kuma bayyana karara cewa wasu ‘kungiyoyin masu sha’awa na musamman’ na kokarin yin magudi tare da bata tsarin diflomasiyya ta hanyar bata sunan masu tattaunawan tare da yin kira ga gwamnatin Amurka da ta gabatar da bukatu mafi tsanani da girma.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments