Mataimakiyar jakadan JMI a MDD ta bukaci kwamitin tsaro na majalisar ya gudanar da taron gaggawa, dangane da hare haren ta’addanci wanda jiragen yakin HKI suka kai kan karamin ofishin jakadancin kasar dake birnin Mamascus babban birnin kasar Siriya. Wanda ya kai ga shahadar manya manyan jami’an dakarun IRGC wadanda suke cikin wurin.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Zahra Ershadi ta bayyana haka ne a cikin wata wasikar da ta rubutawa babban sakataren MDD Antonio Guterres da kuma shugaban kwamitin tsaro na yanzu.
Jami’ar diblomasiyyar ta kara da cewa hare haren na jiya litinin a kan karamin ofishin jakadancin Iran a birnin Damascus ya rusa ginin Ofishin ya kuma kai ga sahadar Janar Muhammad Riza Zahidi da kuma Janar Muhammad Hadi Hajj Rahimi da kuma wasu mutane 5 tare da su.
Ta ce hare haren sun sabawa dokokin kasa da kasa kan diblomasiyya da kuma ma’aikatan diblomasiyya wadanda suka hada da dokar diblomasiyya ta Vienna ta shekara 1961, da ta shekara ta 1963 da kuma wata dangane da wannan ta shekara 1973.
Ershadi ta bukaci kwamitin tsaron ya yi tir da HKI kan kata wadannan dokoki, a lokacinda akwai yiyuwar yakin da ta kunnen a yankin yana iya yaduwa. Sannan ta kammala da cewa Iran tana da hakkin maida martani a duk lokacinda taga ya dace, a inda kuma ya dace.