IRNA- Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa: ta kaddamar da hare-hare da manyan makamai masu linzami kan Isra’ila, domin mayar da martani kan kisan Ismail Haniyyah, Sayyid Hassan Nasrallah da Janar Abbas Nilforoushan.
Tun kafin wannan lokacin dai Iran ta sha alwashin mayar da martani kan kisan Isma’ila Haniyya wanda Isra’ila ta yi kisan gilla a Tehran, inda Iran din ta ce za ta mayar da martanin ne a wuri da kuma lokacin da tag a ya dace.
A ranar Juma’ar da ta gabata kuma Isra’ila ta kai hare-hare a kudancin birnin Beirut, wanda ya yi sanadin shahadar Sayyid Hassan Nasrallah babban sakataren kungiyar Hizbullah, gami da janar Abbas Nilforoushan, jami’in IRGC da yake gudanar da ayyukansa na bayar da shawarwaria Lebanon.
Iran ta kara jaddada cewa dole ne Isra’ila ta fuskanci sakamakon abin da ta aikata na ta’addancin kisan Sayyid Hassan nasrallah da kuma jami’in na IRGc da sauran manyan kwamandojin Hizbullah, da kuma fararen hula da ba su ji ba su gani ba.