Iran: Dan Wasan Motsa Jiki A Gasar “2024 Paris Paralympics” Ya  Sami Lambar Zinari  

A wasan mutsa jiki a gasar ‘2024 Paris Paralimpic’ wanda ke gudana a birnin Paris na kasar Faransa a halin yanzu. Wani dan kasar Iran

A wasan mutsa jiki a gasar ‘2024 Paris Paralimpic’ wanda ke gudana a birnin Paris na kasar Faransa a halin yanzu. Wani dan kasar Iran mai jefa sandar Javelin mai suna Sa’ed Afrooz ya sami lamabar zinari inda ya zo na daya a gasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa Afrooz ya fuskanci yan wasan Javelin na kasashen China, Colombia 2, Morocco, Brazil da kuma Iraki a filin wasannin na birnin Paris inda ya lallasasu gaba daya ya kuma karbi lambar zinari a wannan wasan.

Banda haka Afrooz ya wuce nisan da aka saba a wasannin Paralympic na duniya inda ya jefa sandar Javelin samfurin F34  zuwa nisan mita 40.18, da mita 40.67 da kuma 41.16.  wanda ya wuce na wadanda aka yi a bayan.  Daga karsgen Afrooz ya zama zakara tare da jefa sandar Javelin zuwa nisan mit 41.16.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments