Kasashen Iran da Malaysia Sun soki tallafin makamai da Amurka da wasu kasashen yamma ke ci gaba da baiwa Isra’ila.
Kasashen sun hakikance cewa tallafin da ake baiwa Isra’ila ya sabawa ikirarin da suke yi na kare hakkin bil’adama, hasali yana kawo cikas ga yunkurin tsagaita bude wuta a Gaza.
A wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya litinin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da firaministan Malaysia Anwar Ibrahim, sun tattauna kan batutuwan da suka shafi yankin musamman tattaunawar tsagaita bude wuta a zirin Gaza.
Bangarorin biyu sun jaddada muhimmancin samar da hadin kai a tsakanin kasashen musulmi domin yakar laifukan Isra’ila da kuma kawo karshen kisan kiyashi a zirin Gaza da aka yiwa kawanya.
Sun ce gudanar da taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC zai yi tasiri a wannan fanni.