Iran : An Ayyana Kwanaki Biyar Na Zaman Makoki Bayan Shahadar Nasrallah

A Iran, an ayyana zaman makoki na kwanaki biyar biyo bayan shahadar shugaban kungiyar Hezbollah, ta kasar LebanonSayyed Hassan Nasrallah, wanda ya yi shahada a

A Iran, an ayyana zaman makoki na kwanaki biyar biyo bayan shahadar shugaban kungiyar Hezbollah, ta kasar LebanonSayyed Hassan Nasrallah, wanda ya yi shahada a kazamin harin Isra’ila a kUdancin Beirut ranar Juma’a.

Wannan na kunshe ne a cikin sakon ta’aziyya da jagoran Juyin Juya halin Musulinci na Iran ya fitar bayan sanar da shahadar Sayyed Hassan Nasrallah.

A cikin sakon Jagoran ya ce jagorancin da Sayyed Nasrallah ya yi wa kungiyar ba zai gushe ba  saboda rashinsa ba, hasali ma hakan zai kara tsayin daga daga ‘yan gwagwarmaya.

Ayatullah Khamenei ya bayyana Nasrullah a matsayin babban mayaki, kuma ma’abucin tsayin daka a yankin, malamin addini kuma shugaban siyasa haziki.

Jagoran ya bayyana cewa Nasrallah ya yi shahada a lokacin da yake shirin kare mutanen da ba su da kariya da ke zaune a yankin Dahiyeh da ke kudancin birnin Beirut na kasar Labanon da kuma gidajensu da aka lalata.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa Sayyid Nasrallah ya kwashe shekaru da dama yana gwagwarmaya domin kare al’ummar Falastinu da ake zalunta, daga mamaya, da ruguza gidajensu.

A cikin sakon nasa Ayatullah Khamenei ya ce: “Duniyar musulmi ta yi hasarar babban mutum, haka bangaren gwagwarmaya ya yi rashin wani fitaccen mai rike da tuta, sannan Hizbullah ta Lebanon ta rasa wani shugaba na musamman.”

Jagoran, ya jaddada cewa, ba za a taba rasa albarkar shekaru da dama na hikimar Nasrallah da jihadinsa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments