Makamai masu linzami samfurin Katusha guda uku ne aka cilla kan sansanin sojojin Amurka da ke kusa da tashar jiragen sama na birnin Bagdaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa garkuwan makamai masu linzami na Amurka sun kakkabo biyu daga cikin makaman, amma daya ya fadi a cikin sansanin amma bai jawo wata asara ba.
Labarin ya kara da cewa babu wani ko wata kungiya daga cikin kungiyoyin da basa ga maciji da kasar Amurka a kasar Iraki da ya dauki alkahakin kai hare hare.
Amma dakarun kungiyoyi masu gwagwarmaya da yan ta’adda a kasar ta Iraki wato Hashdushabi sun sha alwashin korar Amurka daga kasarsu, sannan sun sha kaiwa sansanonin sojojin Amurka a Iraki da Siriya hare hare saboda goyon bayan da gwamnatin Amurka take bawa HKI a kissan kiyashin da take yi a Gaza tun farkon watan Octoban shekarar da ta gabata ta.