IMF: Rashin Tabbas Zai Dagula Tattalin Arzikin Duniya

Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko

Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya.

Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya samun karuwar hargitsi a cikin harkokin tattalin arzikin na duniya da dama yake fama da matsala.

Jami’in ya yi bayani ne  bayan sake yin hasashe akan ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda aka fitar a cikin rahoto a ranar Talatar nan.

Asusun bayar da lamunin ya yi hasashen cewa tattalin arzikin duniyar zai bunkasa da kaso 2.8 % a cikin 2025, da hakan yake nuni da koma baya mai tsanani da ya kai 0.5, idan aka kwatantan da hasashen da ya yi a baya a watan Janairu.

Bayan da Amurka ta sanar da Karin kudaden fito akan kayan kasuwanci da ake shigar mata daga kasashen mabanbanta, cibiyoyin kudi na duniya sun yi hasashe, tare da nuni da cewa za a sami koma baya a ci gaban tattalin arzikin na duniya.

Rahoton ya kuma yi gargadi akan  dagula kasuwanci, da hakan zai iya haddasa tsaiko na ci gaba, ko ma haddasa sauyi a hada-hadar kudade.

 Asusun bayar da lamunin na duniya ya yi kira ga kasashe da su bude tattaunawa a tsakaninsu, su kuma samar da daidaito a cikin dokokin kasuwanci, da kiyaye ‘yancin da hada-hadar kudade suke da shi, saboda karfafa tattalin arzikin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments