Search
Close this search box.

Idan Ba A Rusa  “Isra’ila” Ba, To Za Ta Samar Da Abin Koyi Mai Hatsari Ga Duniya

Wani shafi na hanyoyin sadarwa na al’umma wanda kafar watsa labaru ta; “Parstoday’ ta dauka ya bayyana cewa: “ Manyan laifukan da HKI take tafkawa

Wani shafi na hanyoyin sadarwa na al’umma wanda kafar watsa labaru ta; “Parstoday’ ta dauka ya bayyana cewa:

“ Manyan laifukan da HKI take tafkawa sun munana, musamman a wannan zamanin da ake cewa na cigaba ne, kuma sun ketare kowace irin iyaka.”

Marubucin ya kuma kara da cewa; Ta’asar ta Isra’ila ta bai wa duk wasu shaidanu a duniya karfin gwiwar aikata laifuka,don haka duniya ta saurarin mumman abubuwan da za su faru.”

Idan har Isra’ila din za ta aikata abinda take yi a yanzu, wasu ashararan na duniya za su rika yin tambaya, su me zai hana su aikatawa?

A cikin kwanakin bayan nan ne dai sojojin mamayar HKI su ka kai wasu hare-hare akan asibitin “al_Shafa’ tare da tafka laifukan yaki. Haka nan kuma sojojin mamayar sun ci zarafin wata mace musulma a cikin asibitin, kuma a wannan watan na azumin Ramadan mai alfarma.

Ya zuwa yanzu adadin Falasdinawa da HKI ta kashe a cikin watanni 6 na yaki, sun kai 32,000 yayin da wasu da adadinsu ya haura 74,000 su ka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments