OXFOM Ta Bukaci Kasashen G7 Su Tattauna Kan Barazanar Sauyin Yanayi A Taronsu Mai Zuwa

Hukumar OXFOM ta abinci ta kuma MDD ta yi kira ga kasashen mafi karfin tattalin arziki a duniya da su dauki mataki kan wasu al-amura

Hukumar OXFOM ta abinci ta kuma MDD ta yi kira ga kasashen mafi karfin tattalin arziki a duniya da su dauki mataki kan wasu al-amura masu muhimmanci da suke gabanta na sauyin yanayi da kuma yunwa da ke addabar kasashenn duniya a halin yanzu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran, ya nakalto hukumar tana fadar haka, ta kuma kara da cewa kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya dai sun hada da Amurka Jamus, Japan, Faransa Ingila da kuma Canada. Kuma dole ne su hada kai  don fuskantar matsalolin yan gudun hijira, fari da yunwa a wasu kasaashen Afirka da sauyin yanayi ya haddasa. Har’ila yau da basussuka masu nauyi da ke kan kasashe masu tasowa.

 Oxfom ta kara da cewa kauda talauci a duniya, shi ne matsala babba wacce take fuskantar kasashen duniya da dama, kuma shi kadai yana bukatar dalar Amurka biliyon 31 da miliyon 700.

Tace rabon kungiyar G7 na rage talauci a duniya bai fi dalar Amurka biliyon 4 ba ne, wanda kuma bai fi kasha 2.9 na kudaden da kungiyar ta kashe a yaki a shekarar da ta gabata ba. Kungiyar ta kashe dalar Amurla biliyon 1,200 a yaki kadai a shekarar da ta gabata.

Daga karshen Oxfam ta ce manya manyan kasashen duniya suna da hannu a mafi yawan yake yake da zubar da jinni a duniya, amma idan al-amarin ya shafi rage yunwa wanda yake yake suke haddasa,  sai ka ga cewa suna ko in kula da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments