Hizbullah  Ta Cilla  Makamai Masu Linzami Kimana 200 Kan Arewacin HKI

Dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun cilla makamai masu linzami kuma masu yawa a kan arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran

Dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun cilla makamai masu linzami kuma masu yawa a kan arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto bayanan da dakarun kungiyar suka fitar a jiya Alhamis na cewa sun cilla makamai masu linzami kimani 200 kan matsugunan yahudawan da suke arewacin kasar  Falasdinu da aka mamaye, wadanda suka hada da Kiryat Shmona da Akka da Nahariya da wasu wurare kusa da su.

Wata tashar talabijin ta HKI ta bada sanarwan cewa dakarun kungiyar Hizbullah sun cilla makamai masu linzami kimani 100 kan garin Keryat Shmona kadai a jiya Alhamsi wanda shi ne matsugunin yahudawan sahyoniyya mafi girma a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye. Har’ila yau wasu makamai mai masu linzami kimani 50 sun fada kan matsugunan yahudawa da ke Akka da kuma Nahariyya da ke kusa da su.

A ranar laraba ma dakarun Hizbullah sun kai hare hare kan kirtat Shmona inda yahudawa biyu suka halaka.

Sai dai bayan haka da kadan ne jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan kudancin kasar Lebanon da kuma kudancin birnin Beirut inda suka kashe fararen hula da dama a hare haren.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments