Majiyar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa dakarun kungiyar sun kai hare hare da makamai masu linzami sanfurin Fadi-2 kan sansanonin sojojin HKI da kuma wasu matsugunan yahudawan sahyoniyya a safiyar yau Talata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayanan da kungiyar ta fitar a safiyar yau Talat ana cewa a safiyar yau Talata 01-10-2024 sun cillama makaman atilari kan matsugunan yahudawa da ke Shtula.
Banda haka kungiyar ta ce ta cilla makamai masu linzami samfurin Fadi 2 kan sasanin sojojin HKI dake Naqoura a dai dai lokacinda sojojin yahudawan suke kokarin mamayar wasu Karin yankuna a kasar ta Lebanon.
Tun bayan hare haren da jiragen yaki wanda HKI suka kai Dahiya Junubiyya na birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon, wanda ya kai ga shahadar shugaban kungiyar dakarun suka kara yawan makaman da suke cillawa kan yankunnan da yahudawan suka mamaye a arewacin kasar Falasdinu.