Kungiyar Hizbullah ta harba makaman roka na Katyusha a kan wata cibiyar rundunar sojin Isra’ila da ke arewacin Falastinu da yahudawa suka mamaye, a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da take kaiwa yankunan kudancin Lebanon.
Kungiyar Hizbullah ta bayyana hakan ne a wani takaitaccen bayani da ta fitar, ta ce mayakanta sun kai hari a hedikwatar Brigade Golani da ke sansanin tsaunin Neria da makaman roka a safiyar ranar Asabar, inda harin ya samu cibiyar kai tsaye.
Sanarwar ta ce, farmakin ya zo ne domin nuna goyon baya ga Falasdinawa masu tsayin daka a Gaza da kuma bangarorin da ke adawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma daukar fansa kan hare-haren da Isra’ila ta kai kan garuruwa da kauyukan kudancin Lebanon, musamman harin baya-bayan nan da aka kai a kauyen Froun da ke gundumar Bint Jbeil.
A nata bangaren, rundunar sojin Isra’ila ta ce an harba rokoki akalla 30 daga kudancin kasar Lebanon a yankunan da ke arewacin yankunan da aka mamaye.
A halin da ake ciki kuma, an yi ta jin karar harbe-harbe a wasu yankuna da ke kusa da kan iyakar kudancin Lebanon.
Har ila yau kungiyar ta Hizbullah ta sanar a cikin wata sanarwa ta daban cewa ta kai hari kan yankin Hadab Yaron na Isra’ila da makaman atilari.
A ranar Juma’ar da ta gabata, kungiyar Hizbullah ta kai hari kan tashar Ma’ayan Baruch da wani jirgin sama mara matuki dauke da bama-bamai, sannan daga baya a kan barikin Zebdine da gine-gine da na’urorin sa ido a yankunan Metula da Menara na Isra’ila.
Kungiyar ta kuma kai hari a wani wuri a cikin gonakin Shebaa da Isra’ila ta mamaye.
A wannan rana, Hezbollah ta kai hari kan sojojin Isra’ila yankin Abirim da jiragen yaki marasa matuka, a matsayin mayar da martani ga harin da Isra’ila ta kai kan mayakan Hizbullah a garin Kafra da ke kudancin kasar a ranar Alhamis.