Hezbollah ta gurgunta filin jirgin saman Ben-Gurion

Pars Today- Majiyoyi masu alaka da gwamnatin sahyoniyawan sun bayar da rahoton cewa, filin jirgin saman “Ben Gurion” ya gurgunce sakamakon hare-haren kungiyar Hizbullah ta

Pars Today- Majiyoyi masu alaka da gwamnatin sahyoniyawan sun bayar da rahoton cewa, filin jirgin saman “Ben Gurion” ya gurgunce sakamakon hare-haren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana cewa kamfanonin kasashen waje sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da dama zuwa filin jirgin sama na Ben Gurion, filin jirgin saman kasa da kasa mafi girma a yankunan da aka mamaye. A cewar Pars Today da Al-Mayadin ya nakalto, majiyoyin yahudawan sahyoniya sun sanar da soke tashin jirage 50 zuwa filin jirgin saman “Ben-Gurion”.

A sa’i daya kuma, kafofin yada labaru na gwamnatin sahyoniyawan sun kuma ambaci cewa, shafin yanar gizon tashar jiragen sama na “Ben Gurion” ya lalace.

Kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun sanar da cewa, wasu daga cikin jiragen da suka tashi zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion sun sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Ramon, wasu kuma a birnin Alkahira, kuma hakan ya faru ne sakamakon yadda rikicin Hizbullah da Tel Aviv ya yi kamari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments