Sharhin Bayan Labarai: Hare Haren Dakarun Hizbullah Kan HKI A Ranar Lahadi

Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu zai yi Magana a kan maida martanin Sayyid Nasurullah na farko bayan da Natanyahu yayi

Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu zai yi Magana a kan maida martanin Sayyid Nasurullah na farko bayan da Natanyahu yayi nufin fadada yakin da ke faruwa a Gaza zuwa kasar Lebanon.

Matakan kara ruruta wutan yaki wanda Benyamin Natanyahu firai ministan HKI yake  yi a kasar Lebanon a cikin yan kwanakin da suka kawo ya tabbatar da cewa hakan ba zai kawo karshen yaki a yankin ba. Banda haka hare da Natanyahu ya kai kan kasar Lebanon a cikin yan kwanakin da suka gabata sun kara nisantar da batun tsagaita wuta a yankin, kuma yanzun ana batun wuta ne kawai har zuwa abinda hali yayi.

A safiyar Lahadi ce dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon suka yi barin wutan da ba’a saba ba, a yankin arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye har zuwa kusa da birnin Haifa na bakin ruwa.

Dakarun kungiyar sun yi amfani da makamai masu linzami daban dabana. Kungiyar ta bada sanarwan cewa ta yi amfani da makamai masu linzami samfurin Fadi-1 da Fadi-2 a hare haren da ta kai kudancin birnin Haifa. Wanda ya hada da wargaza kamfanin Rafa’el na kera makamai.

Kungiyar ta bayyana cewa wannan itace maida martani na farko ga HKI kan kissan Falasdinawa a gaza da kuma wadanda take kaiwa kan yankuna daban daban a kasar Lebanon a halin yanzu.

Kafafen yada labarai na HKI sun bayyana cewa hizbulla ta kai hare hare da makamai masu linzami har 120 kan wurare daban daban a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye.

Labarin ya kara da cewa a hare harenn safiyar yau Lahadi sun maida hankali kan wuraren soje da kuma masana’antu, kuma sun lalata wurare da dama.

Banda gaka masu aikin kwana kwana suna kokarin kashe gobaran da suka tashi a wurare daban daban a yankin arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye. Sannan gwamnatin HKI ta hana a yada labaran irin asarorin da suke yi sanadiyyar hare haren Hizbullah na safiyar Lahadi.

A cikin wannan halin, wasu kafafen yada labarai na HKI sun bayyana cewa, mafi yawan mutane suna jiran abinda zai zo kasar Lebanon na makaman Hizbullah, amma kuma akwai yiyuwar wasu makaman su zo ta tekun medeteranian.

A yau ne gwamnatin Natanyahu ta shirya gudanar da taron majalisar ministocin kasar amma saboda hare hare masu yawa wanda mayakan Hizbullah suka kai kan arewacin kasar Falasdinu ya sa an dage zaman zuwa wani lokaci, ko kuma sai abinda hali yayi.

A cikin yan kwanakin da suka gabata HKI ta kai hare hare kan masu amfani da na’urar sadarwa ta ‘Page’r da kuma waki toki a kan mutanen kasar Lebanon masu amfani da su, wanda ya kai ga shahadar mutane akalla 37 da kuma raunata wasu kimani 4,000.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah na kasar Lebanon a jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis da ta gabata ya bayyana cewa HKI ta tsallaka dukkan jajayen layin kungiyar don haka a halin yanzu sai abinda fagen fama ya zo da shi wanda zai fayyace matsayin kowa.

Al-amura da dama sun sauya a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye, kuma kungiyar hizbulla ta rikita al-amura da dama a yankin. Daga ciki ta tilastawa yahudawan sahyoniya kimani dubu 300 kauracewa yankin.

A bangaren asarar dukiyoyin kuma an kiyasta cewa HKI tana asarar kimani dalar amurka miliyon 180 a ko wace rana a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments