Hamas Ta Ki Amincewa Da Sabbin Sharudda Da Isra’ila Ta Gabatar

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ba za ta amince da sabbin sharudda daga gwamnatin Isra’ila ba kamar yadda aka bayyana a cikin wata

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ba za ta amince da sabbin sharudda daga gwamnatin Isra’ila ba kamar yadda aka bayyana a cikin wata sabuwar shawara da masu shiga tsakani suka gabatar yayin tattaunawar sulhu a Doha babban birnin kasar Qatar.

Wani jami’in Hamas ya ce bayanan da aka raba wa ‘kungiyar game da sakamakon tattaunawar tsagaita wuta ba su yi daidai da abin da aka amince da shi a shawarwarin Biden ba.

A halin da ake ciki dai manyan jami’ai daga Masar da Qatar da Amurka dake shiga tsakani a tattaunawr sun ce za su sake ganawa a birnin Alkahira kafin karshen mako mai zuwa, da fatan cimma yarjejeniyar kawo karshen mummunan yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, in ji sanarwar hadin gwiwa.

Sanarwar ta ce tattaunawar ta kasance da gaske, mai ma’ana, kuma an gudanar da ita cikin yanayi mai kyau.

Masu shiga tsakani sun dage cewa abin da aka tattauna ya yi daidai da ‘ka’idojin da shugaban Amurka Biden ya gindaya a ranar 31 ga watan Mayu da ya bukaci janye sojojin Isra’ila daga Gaza domin a sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

Masu shiga tsakani za su yi aiki a cikin kwanaki masu zuwa kan cikakken bayani game da shawarar tsagaita wuta a Gaza, a cewar sanarwar, da fatan cimma yarjejeniya bisa sharuddan da aka yanke ranar Juma’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments