Hamas Ta Jinjinawa Colombia Kan Aiwatar Da Matakin Hana Fitar Da Gawayi Zuwa Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinjinawa shugaba Petro na aksar Columbia saboda sake jaddada matakin kasarsa na hana fitar da gawayi zuwa Isra’ila.  A

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinjinawa shugaba Petro na aksar Columbia saboda sake jaddada matakin kasarsa na hana fitar da gawayi zuwa Isra’ila.

 A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce “Muna nuna godiyarmu ga irin jajircewar da jamhuriyar Colombia ta yi na kawo karshen huldar diflomasiyya da yahudawan sahyoniyawan, tare da yin Allah wadai da kisan kiyashin da ‘yan ta’addar yahudawan sahyoniya suke yi kan al’ummarmu a zirin Gaza.” Inji Hamas.

A kasrhen makon jiya ne kasar Colombia a hukumance ta amince da dokar hana fitar da gawayi zuwa Isra’ila a wani mataki na nuna adawa da yakin da Isra’ila ta shafe watanni goma tana yi kan Falasdinawa a Gaza.

Shugaban kasar Colombia Gustavo Petro ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi cewa, “ana amfani da kwal na Colombia wajen kera bama-bamai da ake kashe yaran Falasdinawa.”

Don haka, an haramta “fitar da shi zuwa Isra’ila”, a cewar dokar, wadda ministoci da dama suka sanya wa hannu, ciki har da shugabar gwamnati, Luis Gilberto Murillo, a ranar 14 ga Agusta kuma za ta fara aiki a mako mai zuwa.

Colombia ta kasance daya daga cikin manyan masu samar da kwal wa Isra’ila.

A ranar 1 ga watan Mayu da ya gabata ne shugaban kasar Colombia ya ce kasarsa ta yanke shawarar yanke huldar jakadanci da Isra’ila saboda yakin da ta ke a Gaza tare da katse sayen makamai daga Isra’ilar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments