Hamas, Jihad : Dole Ne Yarjejeniyar Da MDD, Ta Amince Da Ita Ta Kawo Karshen Hare-haren Isra’ila A Gaza

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa Hamas da Islamic Jihad sun gabatar da martani a hukumance game da shawarar tsagaita bude wuta da Majalisar Dinkin Duniya ta amince

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa Hamas da Islamic Jihad sun gabatar da martani a hukumance game da shawarar tsagaita bude wuta da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, suna masu cewa dole ne yarjejeniyar ta kawo karshen duk wasu hare-hare na Isra’ila a zirin Gaza.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyoyin Falasdinawan suka fitar a ranar Talatar sun ce abin da suka sa gaba shi ne kawo karshen ta’addancin da Isra’ila ke ci gaba da yi da kuma muradun Falasdinawa a Gaza.

A cewar majiyoyin Falasdinawa, kungiyoyin masu fafutuka sun gabatar da wasu gyare-gyare kan shawarwarin na Isra’ila, ciki har da wa’adin tsagaita bude wuta na dindindin da kuma janyewar sojojin Isra’ila gaba daya daga Gaza.

Sanarwar da kungiyar Hamas da ta Islamic Jihad suka fitar ta ce, “Amsar tana ba da fifikon muradun al’ummar Palasdinu da kuma wajabcin dakatar da ci gaba da kai hare-hare kan zirin Gaza gaba daya.”

Sanarwar da kasashen Qatar da Masar suka fitar sun ce, “Bangarorin biyu sun tabbatar da cewa, za a ci gaba da kokarin shiga tsakani na hadin gwiwa da Amurka har sai an cimma matsaya, yayin da masu shiga tsakani za su yi nazari kan yadda hada kai da bangarorin da abin ya shafa game da matakai na gaba.”

A ranar Litinin ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shirin tsagaita wuta da Amurka ta gabatar kan Gaza.

Wakilai 14 na Kwamitin Sulhun sun kada kuri’ar amincewa da shawarar tsagaita bude wuta a Gaza, sai kasar Rasha wacce ta kauracewa kada kuri’ar.

Shirin mai matakai uku ya tanadi janyewar sojojin Isra’ila gaba daya daga Gaza, da musayar fursunoni da kuma sake gina yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments