Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce farmakin da Isra’ila ta kai a Rafah zai kawai kara tsananta bala’in jin kai a yankin da aka yi wa kawanya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, kungiyar ta ce kutsen da Isra’ila ta yi a mashigar Rafah na da nufin kawo cikas ga yunkurin tsagaita bude wuta da ake yi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ta hanyar yanke shawarar rufe mashigar Rafah da Kerem Shalom, Isra’ila na jagorantar yankin zuwa ga wani bala’i tare da ci gaba da manufofinta na hadassa yunwa da kuntata wa Falasdinawa.”
Rahotanni sun ce harin na Rafah zai kara raba Falasdinawa sama da miliyan 1, da katse agajin da suke samu a yankin, tare da hana Falasdinawa marasa lafiya da wadanda suka jikkata samun magani a wajen yankin da aka yi wa kawanya.
Kutsen ya zo ne bayan Hamas ta ce ta amince da shawarar tsagaita bude wuta da masu shiga tsakani Qatar da Masar suka gabatar. Sai dai gwamnatin ta ce yarjejeniyar da aka tsara ta gaza biyan bukatunta.
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta ce Benjamin Netanyahu yana la’akari ne kawai da muradun kansa da kuma majalisar ministocinsa masu tsattsauran ra’ayi.
Hamas ta dorawa Amurka alhakin ci gaba da yakin Isra’ila
A halin da ake ciki kuma, Nabil Abu Rudeineh, mai magana da yawun hukumar Falasdinu, ya yi kira ga Amurka da ta matsa wa Isra’ila lamba ta yi watsi da mamayar Rafah. Ya ce mamayar na barazanar rubanya wahalhalun da al’ummar Gaza ke ciki.
Isra’ila ta ce za ta zafafa hare-hare a Rafah da ke kudancin Gaza har sai ta fatattaki Hamas, ko kuma an sako wasu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.
Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce kodayake sabon daftarin tsagaita wuta da Hamas ta amince da shi bai biya bukatun gwamnatinsa ba, za ta ci gaba da tattaunawa.