Hamas : Ba Wata Shawarar Tsagaita Wuta, Idan Isra’ila Ta Ki Janye Sojoji Daga Philadelphi

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce babu bukatar wata sabuwar shawarar tsagaita wuta, muddin Isra’ila ta ki

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce babu bukatar wata sabuwar shawarar tsagaita wuta, muddin Isra’ila ta ki janye sojoji daga Philadelphi.

Hamas ta caccaki Netanyahu, tana mai cewa matakin da ya yanke na kin janye sojoji daga Philadelphi Corridor na da nufin dakile duk wani kokari na cimma yarjejeniyar sulhu da musayar fursunoni, tana mai cewa lokaci ya yi da za a matsa lamba kan Isra’ila.

Shi dai Titin Philadelphi wanda wani karamin fili ne da ke tsakanin Masar da Falasdinu da aka fi sani da Saladin Axis, ya kasance a yanzu wani karfen kafa a tattaunawar Isra’ila da Falasdinu.

Hakan na zuwa ne bayan Netanyahu ya jaddada kin amincewarsa na janyewa daga titin, yana mai ikirarin ba tare da wata hujja ba cewa kungiyar gwagwarmayar Hamas za ta iya kwashe mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su daga kudancin Gaza.

Masu suka sun ce kin janyewar Netanyahu daga titin ya dagula yarjejeniyar musayar fursunoni da Hamas.

Tunda farko dai wani babban jami’in Amurka ya ce idan sojojin Isra’ila suka janye daga yankin Philadelphi Corridor, “akwai abubuwan da Amurka za ta iya yi domin bai wa Isra’ila cikakken bayanin tsaron da take bukata.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments