Gwamnatin Najeriya Ta Kare Kanta Game Da Karin Farashin Man Fetur

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce karin kudin man fetur da aka yi zai taimaka wa Nijeriya wajen ci gaban tattalin arziki. Tinubu ya

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce karin kudin man fetur da aka yi zai taimaka wa Nijeriya wajen ci gaban tattalin arziki.

Tinubu ya bayyana haka ne a China lokacin da yake ganawa da ‘yan Nijeriya mazauna China ranar Juma’a.

“Nijeriya na fuskantar sauye-sauye, kuma muna daukar muhimman matakan da suka dace,” a cewar shugaban, kamar yadda wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar ta bayyana.

Tinubu ya ce dole ne gwamanati ta dauki tsauraran matakai in har ana so ƙasar ta bunƙasa.

Ya kuma bayyana cewa samar da kayan more rayuwa kyauta ko cikin farashi mai sauƙi babu abin da zai yi sai kara jefa ‘yan ƙasa cikin wahala.

“Daga lokacin da kuke son samun abu kyauta, to a lokacin ne abubuwan za su kara tsada, sannan a samu jinkiri wajen samun ci gaba mai ma’ana.

Taron da Tinubu ya yi da ‘yan Nijeriya a China shi ne abu na karshe da ya yi a ziyarar da ya kai don taron China da shugabannin Afirka , kafin tafiyarsa Dubai, inda daga nan kuma zai wuce zuwa Birtaniya, a cewar sanarwar ta fadar shugaba kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments