Leadership–Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙaddamar da rabon takin buhu dubu ɗari da ashirin (120,000) ga al’ummar ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa.
Rabon takin wanda aka gudanar da shi a harabar makarantar Firimare dake Kawo, ya samu halarcin manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa da kuma masu sanya ido.
Da yake jawabi yayin rabon takin, mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Kaduna, Malam Ibrahim Ibrahim, ya bayar da tabbacin cewa duk waɗanda hukumar bunƙasa aikin Gona ta jihar ( KADA) ta wallafa sunayensu za a tabbatar da cewa sun samu taki kamar yadda Gwamnatin Jihar ta tsara.
Malam Ibrahim, ya ƙara jaddada ƙudirin Gwamnatin Jihar wajen tallafawa cigaban rayuwar al’ummar jihar ta ɓangarori da dama yana mai ba su tabbacin cewa al’ummar jihar Kaduna zasu amfana da romon mulkin dimokuraɗiyyar Gwamnatin Uba Sani.
Allummar mazaɓun unguwar Sarki da Kawo da hayin Banki da Badarawa da Kuma unguwar Dosa sune aka rabawa takin. A cewarsa, rabon takin ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa shi ne mafi tsari a faɗin jihar kaduna.