Gwamnatin Amurka Ta Musanta Cewa: Gwamnatin Isra’ila Tana Aiwatar Da Laifukan Yaki A Gaza

Gwamnatin Amurka ta ce: Ba ta ganin akwai laifukan yaki ko kisan kare dangi da ake yi Gaza kuma tana yin tir da zarge-zargen Majalisar

Gwamnatin Amurka ta ce: Ba ta ganin akwai laifukan yaki ko kisan kare dangi da ake yi Gaza kuma tana yin tir da zarge-zargen Majalisar Dinkin Duniya kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila

Gwamnatin Amurka ta yi furuci da cewa: Babu wani dalili da wani kwamiti na musamman na Majalisar Dinkin Duniya zai nuna cewa: Ayyukan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a yakin da take yi kan Zirin Gaza ya dace da halayen kisan kiyashi.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Vedant Patel ya shaida wa manema labarai cewa: Wannan wani abu ne da Amurka bata yarda da shi ba kwata-kwata, ya kara da cewa: Sun yi imanin cewa: Ire-iren wadannan maganganu da kuma zarge-zarge kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba su da tushe balle makama.

Patel ya yi tir da rahoton da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta buga a jiya Alhamis, inda ta tabbatar da cewa ta tattara shaidun da ke nuna cewa jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila na aikata laifukan yaki kan Falasdinawa ta hanyar tilasta musu yin gudun hijira daga muhallinsu, da kuma cewa: Ayyukan sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi daidai da fassaran kawar da wata al’umma daga kan doron kasa.

Patel ya jaddada cewa: Tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira zai zama jan layi ga Amurka kuma ya saba wa ka’idojin da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya gindaya a nisance shi tun farkon bullar yakin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments