Ghana Za ta Haramta Fitar Da Albarkatun Da Ba A Sarrafa Ba

gwamnatin kasar ghana za ta hana fitar da albarkatun da baa sarrafa ba zuwa kasashen waje

Shugaban Ghana, John Dramani Mahama,ya ce kasar za ta haramta fitar da dukkan wasu albarkatun ƙasa waɗanda ba a sarrafa ba zuwa kasashen waje nan da shekarar 2030 domin ganin ana tace su a cikin gida.

A hirar da ya yi da wata mujallar tattalin arziki, shugaba Mahama ya ce wannan umurni zai shafi muhimman albarkatun da suka haɗa da ma’adinin bauxite, manganese, lithium, danyen karfe da zinare, da cocoa, lamarin da ke nuna gagarumin sauyi zuwa ga tsarin ƙishin albarkatun ƙasa a fadin Yammacin Afirka.

Wannan manufa ta faɗaɗa haramcin da ke akwai a halin yanzu wanda ya shafi tsofaffin ƙarafa da waɗanda ba ɗanye, inda hakan zai tilasta wa ƙasar mai ɗimbin arziƙin zinare a Afirka sauyawa gabaɗaya daga fitar da albarkatun da ba a sarrafa ba zuwa tace su a cikin gida don samun cikakkiyar daraja.

Domin daidaita ɓangaren aikin gona da a halin yanzu yake fuskantar matsananciyar matsalar kuɗi, gwamnati za ta kuma bukaci masana’atun cikin gida su tace akalla kashi 50 na dukkan ƙwayoyin koko da aka noma a kasar, wanda hakan ya ƙaru sosai idan aka kwatanta da kashi 30 zuwa 40 da ake tacewa a halin yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted