Gwamnatin Shugaban kasa John Mahama ta tsige Gertrude Torkornoo daga mukaminta na babbar mai shari’ar kasar, bisa wasu zarge-zarge da ake yi mata, domin bayar da damar gudanar da bincike.
Matakin da gwamnatin ta dauka na tsige babbar mai shari’ar ya jawo cece-kuce a tsakanin mutanen kasar.
Tsohon mai shigar da kara na kasar Godfrred Yeboah Dame ya yi tir da matakin na gwamnati da ya siffata da farmaki mafi girma akan ma’aikatar shari’a a tarihin kasar.”
Ita kuwa jam’iyyar hamayya ta zargi shugaban kasa da tsoma baki a harkokin shari’ar kasar, domin nada alkalan da za su zama masu biyayya ga jam’iyyar da take Mulki ta ( NDC).
Torkornoo da ta hau mukamin nata a 2023, kuma ta kasance mace ta uku da ta rike wannan mukamin a tsawon tarihin ma’aikatar shari’ar kasar. Har ya zuwa yanzu dai ba ta ce komai ba akan tuhume-tuhumen da ake yi ma ta.