Ghana Na Kokarin Fara Amfani Da Fasahar Nukiliya

Ghana ta sa hannu kan wata yarjejeniyar samar da nukiliya ta hanyar amfani da fasahar makamashin NuScale da wani kamfanin Amurka, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin

Ghana ta sa hannu kan wata yarjejeniyar samar da nukiliya ta hanyar amfani da fasahar makamashin NuScale da wani kamfanin Amurka, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana a ranar Alhamis, a daidai lokacin da ƙasar ke yunƙurin kafa tashar makamashin nukiliya ta farko.

Kamfanin Makamashin Nukiliya na Ghana da Regnum Technology Group na Amurka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tura wata karamar na’urar sarrafa makamashin NuScale VOYGR-12 (SMR) zuwa babban taron Amurka da Afirka kan makamashin nukiliya a Nairobi.

Na’urorin SMRs dai sun fi kankanta idan aka kwatanta da irin wadanda ake amfani da su a yanzu, kuma ana iya kera su a masana’anta. Amma akwai tambayoyi masu yawa game da ko za a ringa kasuwancinsu.

Amurka na koarin inganta fasahohin da take dauka a matsayin makamashi mara gurɓata muhalli, kana ta sayar da su ga ƙasashe masu tasowa.

Gwamnatin Shugaba Joe Biden ta yi imanin cewa makamashin nukiliyar da ke samar da wutar lantarki kusan babu hayaki a ciki, sannan yana da matukar tasiri wajen yaki da sauyin yanayi.

Makamashin nukiliya, a daya bangaren kuma yana samar da sharar nukiliya ta dindindin.

Kamfanin NuScale shi kaɗai yake da lasisin kera na’urar SMR a Amurka. A bara ne ya soke aikinsa ɗaya tilo a Amurka saboda hauhawar farashi.

Sauran takwarorin kamfanin da suka nemi aikin sun hada da kamfanin EDF na kasar Faransa da kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta China, kamar yadda wani jami’in ma’aikatar makamashi a Ghana ya bayyana a watan Mayu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments