Benjamin Netanyahu Da Yoav Gallant Sun Buya A Karkashin Rami A lokacin Hare-Haren Iran

Sharhin bayan labaran namu zai yi magana ne kan matakin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauka na mayar da martani kan kisan gillar da

Sharhin bayan labaran namu zai yi magana ne kan matakin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauka na mayar da martani kan kisan gillar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa Isma’il Haniyya shugaban bangaren siyasar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a birnin Tehran ta hanyar harba jerin makamai masu linzami kan haramtacciyar kasar ta Isra’ila, yayin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da ministan yakinsa Yoav Gallant suka shige ramin karkashin kasa domin tsira da rakansu kamar burage, da ni Sunusi Wunti zan jagoranci gabatar muku da shirin kamar haka:-

A yayin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke harba jerin makamai masu linzami kan haramtacciyar kasar Isra’ila a ranar Talatar da ta gabata da yamma, Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da ministan yakinsa sun tsere zuwa maboyar karkashin kasa domin tsira da rayukansu.

Tashar talabijin ta 13 ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya shafe sa’o’i da dama tare da wasu ministocin gwamnatinsa a wani maboyar karkashin kasa a birnin Kudus domin neman tsira da rayuwarsu.

Yayin da Ministan Yaki na gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila, Yoav Galant, ya kasance a wani ramin karkashin kasa a ma’aikatar yaki haramtacciyar kasar Isra’ila da ke birnin Tel Aviv fadar mulkin yahudawan sahayoniyya.

Mazauna yankin sun ce: Netanyahu bai kuskura ya fuskanci yahudawan sahayoniyya ba, kuma sun kasance suna mamakin inda ya shiga bayan sa’a guda na hare-haren bama-baman da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai kan birnin Tel Aviv?

A cewar kafar yada labaran yahudawan sahayoniyya, sojojin gwamnatin mamaya sun yi furuci da cewa: Lallai makamai masu linzami na Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun ruguza gine-gine da kuma wuraren kula da jiragen yaki a sansanonin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Mahukuntan gundumar Hod Hasharon dake arewacin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila, sun sanya ido kan yadda hare-haren suka ruguza tare da lalata gidaje kusan 100 sakamakon harin mayar da martanin da makamai masu linzami da kasar Iran ta harba a yammacin ranar Talata.

Hukumar yada labaran Isra’ila ta rawaito karamar hukumar na cewa kimanin gidaje 100 ne suka ruguje ko lalacewa a birnin bayan binciken ire-iren barnar da hare-haren makamai masu linzami.

A ranar Talata ne Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suka yi luguden makamai masu linzami kan haramtacciyar kasar Isra’ila lamarin da ya janyo hasarar rayukan yahudawan sahayoniyya da tarwatsa kayan aiki da kuma Sanya rufe sararin samaniyar haramtacciyar kasar baya ga tserewar miliyoyin yahudawan sahayoniyya zuwa maboyar karkashin kasa, a yayin da ake jin karar wusur din gargadi a duk fadin haramtacciyar kasar Isra’ila kan kowa ya shige mafakar ramukan karkashin kasa domin tsira da rayuwarsa.

Hare-haren makamai masu linzamin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan haramtacciyar kasar sun zo ne a matsayin mayar da martani ga kisan gillar da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa shugaban tsohon ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Isma’il Haniyyeh a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran a karshen watan Yulin wannan shekara, haka nan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta aiwatar da kisan gilla kan babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah da kwamandan Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran, Abbas Nilforshan, a wani samame da ta kai a kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon a ranar 27 ga watan Satumba.

A cewar masu lura da al’amuran yau da kullun, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kasance tana boye ire-iran hasarorin da hare-haren kasar Iran suka haifar kanta, haka nan hasarorin rayukan da ta yi a Zirin Gaza da kuma kasar Labanon, sannan tana hana ‘yan jaridu daukar hoto da yada hotunan a faifan bidiyo, tare da yin gargadi kan hakikanin abin da yake faruwa a duk wani bayanin kafafen yada labarai na cikin haramtacciyar kasar Isra’ila da na waje, sai dai bayanan da ta sanar da kafafen yada labarai da ke karkashin ikonta.

Kashi 90 cikin dari na makamai masu linzami da ake harbawa a gagaruman hare-hare kan haramtacciyar kasar Isra’ila suna isa wurin da aka sai ta su, wanda jami’an yahudawan sahayoniyya suke kore isarsu wuraren da akai hare-haren, kuma wannan hare-hare na Jamhuriyar Musulunci ta Iran shi ne irinsa na biyu a cikin kimanin watanni 6 da suka gabata.

Babban hafsan hafsan sojin Iran Manjo Janar Mohammad Baqiri ya bayyana cewa: Za su sake kai hare-hare masu karfi da tsanani kan haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma zasu kai hari kan dukkanin kayayyakin more rayuwa na yahudawan sahayoniyya idan har gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila) ta yi gigin mayar da martini kan kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments