Fira Ministan Kasar Spain Ya Bukaci Duniya Da Daina Sayar Wa ‘Yan Sahayoniyya Makamai

Kasar Spain ta yi kira ga kasashen duniya da su daina sayar da makamai ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya Fira ministan kasar Spain

Kasar Spain ta yi kira ga kasashen duniya da su daina sayar da makamai ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya

Fira ministan kasar Spain Pedro Sanchez a yau Juma’a ya bukaci kasashen duniya da su daina sayar da makamai ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai yin Allah wadai da hare-haren da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar kan Dakarun kai daukin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya na “UNIFIL” da suke kudancin kasar Lebanon.

A bayan ganawarsa da PaparomaFrancis a fadar Vatican na Mabiya addinin Kirista, Sanchez ya yi kakkausar suka kan yadda hare-haren haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da janyo tabarbarewa al’amura a yankin Gabas ta Tsakiya. Fira ministan na kasar Spain ya ce: A ba shi dama a wannan mataki ya yi soka tare da yin Allah wadai da hare-haren da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Lebanon.

Sanchez ya yi kira ga kasashen duniya da su yi koyi da kasar Spain da ta daina sayar wa haramtacciyar kasar Isra’ila makamai tun a watan Oktoban shekara ta 2023, da nufin hana ci gaba da ruruwar wutar tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments