Falasdinawa Suna Gudanar Da Yajin Aiki Kan Kisan Kiyashin Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Falasdinawa sun shiga yajin aikin gama gari a Gabar Yammacin Kogin Jordan sakamakon kisan kiyashin yahudawan sahayoniyya a birnin Tulkaram Jami’an hukumar Falasdinawa a gabar

Falasdinawa sun shiga yajin aikin gama gari a Gabar Yammacin Kogin Jordan sakamakon kisan kiyashin yahudawan sahayoniyya a birnin Tulkaram

Jami’an hukumar Falasdinawa a gabar yammacin kogin Jordan sun sanar da fara yajin aikin gama gari a jiya Juma’a a wasu jahohin Falasdinu daban-daban, domin nuna alhininsu kan shahadar Falasdinawa 18 a kisan gillar da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a sansanin ‘yan gudun hijirar birnihn Tulkaram a yammacin ranar Alhamis.

Al’ummar Gabar Yammacin Kogin Jordan sun yi kiran fitowa zanga-zangar nuna bacin rai da alhini a dukkanin larduna, da kara kaimi a fagen kalubalantar ‘yan mamaya da suke cikin yankunan Falasdinawa, domin kare kasa da wurare masu tsarki da kuma manufofin kasar Falasdinu.

A sanarwar da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta fitar ta ce: A yayin da suke jimamin shahadan Falasdinawa da aka aiwatar da kisan kiyashin kan su a birnin Tulkarm sakamakon hare-haren bama-bamai na sojojin ‘yan mamaya, kungiyar Hamas tana da tabbacin cewa: ‘Yan gwagwarmayar Tulkaram da dukkan hukumomin yankin gabar yammacin kogin Jordan za su ci gaba da tsayin daka wajen ganin sun karya azamar ‘yan mamaya, kuma bakar siyasar aiwatar da kashe-kashe ba za ta yi nasara ba wajen kawar da al’umma daga kan zabinsu na arangama da tsayin daka a kan ja’irar gwamnatin ‘yan mamaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments