Erdogan : Dole Ne A Hana Isra’ila Jefa Yankin Cikin Yaki  

Shugaban kasar Turkiyya ya ce dole ne a hana Isra’ila “jefa yankin gaba daya cikin yaki,” yana mai gargadin kasashen yammacin duniya kan goyon bayan

Shugaban kasar Turkiyya ya ce dole ne a hana Isra’ila “jefa yankin gaba daya cikin yaki,” yana mai gargadin kasashen yammacin duniya kan goyon bayan da suke bai wa gwamnatin kasar.

Erdogan, wanda ke magana a wani taron manema labarai a Ankara tare da shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi, ya ce wasu yankuna na ci gaba da ba da “goyon baya ga Isra’ila”.

A Don haka “Suna da hannu a laifukan da kisan kiyashin da ake yi wa farar hula na Gaza.”

Erdogan ya ce gwamnatin Isra’ila, baya ga jefa dubban ton na bama-bamai kan fararen hula, tana ci gaba da gudanar da yakin yunwa a Gaza.

Shi kuwa a nasa bangare Shugaban Masar ya ce halin da ake ciki a Gaza wani bala’i ne da ba a taba ganin irinsa ba.

Sisi ya kuma yi kira da a “dakatar da ta’azzara lamarin a Yammacin Kogin Jordan”, da Isra’ila ke yi tun makon jiya.

“Na sake jaddada matsayar Masar da Turkiyya na yin kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa, tare da yin watsi da farmakin da Isra’ila ke yi a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, da kuma daukar kwararan matakai don cimma burin al’ummar Falasdinu na kafa kasarsu mai cin gashin kanta bisa dogaro da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta,” in ji shi.

A yayin taron, wanda shi ne karon farko a irin wannan ziyara da wani shugaban Masar ya kai tsawon shekaru a Ankara, bangarorin biyu sun ce suna son zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments