ECOWAS Zata YI Taro A Ghana Don Tattauna Batun Niger, Mali Da Burkina Faso

Kungiyar raya tattalin arziki ta kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fara taro a kasar Ghana don tattauna al-amura da suka shafi kasashen Niger Burkina Faso

Kungiyar raya tattalin arziki ta kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fara taro a kasar Ghana don tattauna al-amura da suka shafi kasashen Niger Burkina Faso da kuma Mali.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa agendar taron nasu na kwanaki biyu, sun hada da huldar kungiyar da kasashen uku, musamman cibiyoyin ECOWAS da suke cikin kasashen, sannan da batun kudaden fito na kashi 0.5% wanda kungiyarsu ta (AES) ta dorawa kayakin da suke shigowa  kasashensu da sunan gudanar da kungiyarsu. Labarin yace kungiyar ECOWAS bata karban kudaden fito da Visa  daga kasashen kungiyar gaba daya tun kafin kasashen uku su fita amma a halin yanzu su suna karba. Kasashen uku sun bayyana ficewarsu daga ECOWAS ne daga farkon wannan shekarar.

Daga karshe kungiyar ta bayyana cewa zata fidda tsarin tattaunawa da kasashen uku daya bayan daya don warware matsalolin da ficewar daga kungiyar suka haddasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments