Rahotanni sun bayyana cewa da safiyar yau Litinin dubban daruruwan Alummar kasar Nejar ne suka yi zanga-zangar a gaban sansanin sojojin Amurka dake arewacin kasar kuma sun yi ta rera taken neman sojojin Amurka su gaggauta ficewa daga kasarsu
Ko a jiya ma masu zanga zangar sun yi jerin gwano a gaban sansanin sojojin Amurka dake garin Agadaza a arewacin kasar ta Nijar domin nuna rashin amincewarsu da ci gaba da zaman sojojin mamaya na Amurka a kasarsu,
Fira ministan kasar ta Nijer Ali lamini Zain da kuma Kurt Kampel mataimakin ministan harkokin wajen Amurka sun cimma matsaya kan batun rattaba hannu kan jadawalin lokacin ficewar sojojin Amurka daga kasar ta Nijer
Nijer na taka muhimmiyar rawa a ayyukan da sojojin Amurka ke gudanarwa a yankin Sahel , kuma ita ce ke dauke da babban sansanin sojojin saman Amurka .