Brigadier General Ali Mohammad Naeini, kakakin dakarun dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar ya bayyana cewa dakarunsa a shirye suke fiye da ko wani lokaci wajen kara kan iyakokin JMI daga makami.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran Naeini yana fadar haka a yau Talata a wani taro da kafafen yada labarai a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa a dai-dai lokacinda kasar ta cika shekaru 46 na nasarar juyin juya halin musulunci a kasar dakarun na IRGC suna cikin shirin da basu taba irinsa ba don kare kan iyakokin JMI.
Kafin haka, a farkon wannan watan jami’an gwamnatin JMI sun bayyana cewa kasar tana cikin shiri mai kyau na kare kan iyakokin kasar mai tsarki, sannan daga karshe sun bayyana cewa tsaron kasar jan layi ne ga makiya, don haka makiya sun yi hattara, kuma babu tattaunawa kan sa.