Bullar Sabuwar Dambaruwar Siyasa Zata Lalata Alakar Kasashen Aljeriya Da Faransa

Wani mummunan rikici ya sake kunno kai da zai iya lalata alakar da ke tsakanin kasashen Aljeriya da Faransa Rahotonni sun watsa labarin cewa: Wani

Wani mummunan rikici ya sake kunno kai da zai iya lalata alakar da ke tsakanin kasashen Aljeriya da Faransa

Rahotonni sun watsa labarin cewa: Wani sabon rikici da ya barke tsakanin kasashen Aljeriya da Faransa ya tunkari lalata alakar da ke tsakanin kasashen biyu, yayin da Aljeriya ta sanar da janye jakadanta a birnin Paris cikin gaggawa sakamakon amincewar da gwamnatin Faransa karkashin shugabancin Emmanual Macron ta yi cewa: Yankin Yammacin Sahara mallakin Kasar Maroko ne.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ta fitar ta bayyana cewa: Gwamnatin Aljeriya ta yanke shawarar janye jakadanta daga kasar Faransa, bayan matakin da gwamnatin Faransa ta dauka na bayyana cikakken goyon bayanta ga abin da ta kira tabbatar da mulkin mallaka kan yankin yammacin Sahara.

Sanarwar ta kara da cewa: Wannan amincewa da kasar Faransa ta yi na mulkin mallaka kan yankin yammacin sahara, tana matsayin keta hakki na kasa da kasa, tare da kin amincewa da ‘yancin al’ummar Yammacin Sahara na cin gashin kansu, kuma Faransa ta sabawa duk wani kokari da Majalisar Dinkin Duniya ke yi na warware matsalar yankin yammacin na Sahara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments