Search
Close this search box.

Asusun Kula Da Mata Da Kana Nan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF Ta Bukaci A Kawo Karshen  Laifukan Isra’ila A Gaza.

A wani martani da Asusun kula da mata da yara kanana na majlisar dinkin duniya UNICEF ya yi game da shahadar yara dama a yankin

A wani martani da Asusun kula da mata da yara kanana na majlisar dinkin duniya UNICEF ya yi game da shahadar yara dama a yankin Gazza sakamakon lugudan wuta da Isra’ila ke ci gaba da yi a yankin Gaza  ta bukaci a gaggauta kawo karshen kisan kiyashin Isra’ila cikin gaggawa.

Wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da kafafen watsa labaran falasdinu suka fitar da wata sanarwa na hare haren da sojojin HKI suka kai a  Rafah dake kudanci Gaza inda falasdinawa 19 ciki harda yara 14 yayin da wani adadi mai yawa kuma suka jikkata.

Sanarwar baya bayan nan da ma’aikatar lafiya ta yankin falasdinu ta fitar ya nuna cewa  daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 da ta gabata zuwa yanzu bayan kaddamar da harin Isra’ila  a yankin gaza kimanin mutane 34 da 97 ne suka yi shahada yayin da mutane dubu 76 da da 901 ne suka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments