Arakci: Mun Yi Tattaunawa Mai Kyau Da Mahukuntan Kasar China

Ministan harkokin wajen Iran wanda ya ziyarci kasar China, ya bayyana cewa, tattaunawa da mahukunta wannan kasa ta yi kyau, kuma ba da jimawa ba,

Ministan harkokin wajen Iran wanda ya ziyarci kasar China, ya bayyana cewa, tattaunawa da mahukunta wannan kasa ta yi kyau, kuma ba da jimawa ba, shugaban kasar Iran zai kai Ziyara can kasar.

Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci bayan ganawa da takwaransa na China ya ce; Na yi doguwar ganawa da ministan harkokin wajen China, wacce take mai muhimmanci, kuma kusan dukkanin bangarorin da suka shafi alakar tsakanin kasashenmu biyu mu ka tattauna, haka nan kuma batutuwa da su ka shafi siyasar kasa da kasa.”

Arakci ya kara da cewa; Da akwai fahimtar juna a tsakaninmu, musamman abinda ya shafi batun makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, da tataunawar da ake yi da Amurka.”

Haka nan kuma ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da su ka tattauna da su ka hada siyasar Amurka da halayyarta ta nuna karfi, da kokarin da take yi na mamaye fagen siyasar kasa da kasa.

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma yi Magana akan ziyarar da shugaban kasar Iran zai kai zuwa kasar China wacce za ta kasance ba da jimawa sosai ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments