Araghchi : Saudiyya Na Da Mahimmanci Na Musamman A Manufofin Ketare Na Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi, ya jaddada mahimmanci na musamman da kasar Saudiyya take da shi a cikin manufofin ketare na kasar Iran,

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi, ya jaddada mahimmanci na musamman da kasar Saudiyya take da shi a cikin manufofin ketare na kasar Iran, inda ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Tehran da Riyadh na samun ci gaba mai kyau.

A cikin wata hira da ta yi da tashar Al-Sharq ta Saudiyya a baya-bayan nan, Araghchi ya bayyana cewa, an fara hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu a hukumance, wanda ke nuna wani sabon mataki na huldar diflomasiyya.

Araghchi, wanda ya raka shugaba Masoud Pezeshkian a ziyarar aiki a kasar Iraki, ya bayyana kalubalen da kasashen biyu suka fuskanta a baya, amma ya yabawa kasashen Iraki da Sin wajen taimaka wajen farfado da huldar dake tsakanin kasashen biyu.

“A baya mun sha fama da takaddama da Saudiyya, amma ta hanyar shiga tsakani na Iraki, da kuma Sin daga bisani, mun dawo da dangantakarmu, kuma a cikin ‘yan shekarun baya bayan nan, dangantakar ta ci gaba da bunkasa.”

Har ila yau, ya yi ishara da tattaunawar siyasa da ke gudana tsakanin Tehran da Riyadh, inda ya bayyana cewa, a halin yanzu kasashen biyu suna tuntubar juna kan harkokin yankin, wanda wani gagarumin sauyi idan akayi la’akari da dangantakar da ta yi tsami a baya.

Ya jaddada cewa manufofin harkokin wajen Iran a karkashin gwamnatin shugaba Pezeshkian na mayar da hankali ne kan karfafa alaka da kasashe makwabta.

Araghchi ya kuma jaddada wajabcin kulla alaka mai karfi tsakanin Iran da Saudiyya domin samar da zaman lafiya a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments