An Shiga Kwana Na Biyu A Zanga-zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya

A Najeriya an shiga kwana na biyu na zanga zangar gami gari game da yunwa da tsadar raruwa a kasar mafi yawan jama’a a najhiyar

A Najeriya an shiga kwana na biyu na zanga zangar gami gari game da yunwa da tsadar raruwa a kasar mafi yawan jama’a a najhiyar Afrika.

A jiya an gduanar da zanga zangar a sassa daban daban na kasar.

To saidai bayanai sun ce zanga zangar ta rikide zuwa tarzowa biyo bayan da wasu masu zanag zangar sukayi ta fasa shaguna da cibiyoyin gwamnati.

‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zamga zangar.

Gwamnatocin jihohin da dama sun sanya dokar hana fita, a wani yunkuri na dakile tarmozar.

Jihohin da suka saka dokar sun hada da Kano, Borno, Yobe, Jigawa da kuma Katsina, a yayin da Abuja aka takaita yawan masu zanga zangar.

Ranar farko ta zanga-zangar da aka fara a Nijeriyar jiya Alhamis ta bar baya da kura, inda rahotanni daga sassan kasar suke nuna yadda aka samu asarar rayuka da dukiyoyi, da kuma barnata kadarorin gwamnati da ma na al’umma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments