An Rantsar Da Mahamat Deby A Matsayin Sabon Shugaban Kasar Chadi

Zababen shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby, ya yi, rantsuwar kama aiki a matsayinsa na shugaban kasara yau Alhamis. An yi bikin rantsar da shi

Zababen shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby, ya yi, rantsuwar kama aiki a matsayinsa na shugaban kasara yau Alhamis.

An yi bikin rantsar da shi tare da halartar manyan baki daga kasashe ketare.

“Daga yanzu, ni ne shugaban ‘yan kasar Chadi,” in ji Mahamat Idriss Deby, a jawabin rsantsar da shi.

Ga wadanda ba su zabe shi ba, Shugaban kasar ya nuna cewa yana mutunta wannan ‘yancin, “wanda yake nufin ci gaban dimokuradiyyar mu”.

Mahamat Idriss Deby, ya yi rsantuwar ne bayan lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 6 ga watan Mayu, wanda hakan ya kawo karshen mulkin rikon kwarya da aka shafe shekara uku ana gudanarwa a kasar, bayan rasuwar mahifinsa Idriss Deby Itno a fagen daga.

Hukumar zaben kasar ce ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da samu da kashi 61 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada.

Saidai jam’iyyun adawan kasar ciki har da babban abokin hamayyarsa firaminista, Succes Masra suka yi watsi da shi, suna masu ikirarin cewa akwai kura-kurai a ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments