Kungiyar agajin Falasdinawa ta sanar da gano wasu gawawwaki shahidai 50 a wani babban kabari a harabar asibitin “Nasir” dake Khan Yunus wanda ‘yan sahayoniya su ka binne su a ciki.
A cikin kwanaki biyu da su ka gabata an gano wasu gwamman gawawwakin shahidan a harabar wannan asibitin, da hakan ya sa adadin wadanda sojojin sahayoniya su ka yi wa kisan kiyashi ya ka 283.
Ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahadi bisa kididdigar ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa sun haura dubu 34 da 183. Wadanda su ka jikkata kuwa sun kai dubu 77 da 143.
Gano sabbin gawawwakin dai na Falasdinawa yana zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Amurka ta bai wa HKI taimakon makamai da kudinsu su ka kai dala biliyan 26.