An Bude Taron Kolin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka FOCAC 2024

Yau Alhamis, an bude taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC na shekarar 2024 a birnin Beijing. Cikin jawabinsa, na

Yau Alhamis, an bude taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC na shekarar 2024 a birnin Beijing.

Cikin jawabinsa, na bude taron Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya bayyana cewa, kafuwar dandalin na FOCAC a shekarar 2000 yana da muhimmanci matuka wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka.

Cikin shekaru 24 da suka gabata, kasar Sin da kasashen Afirka sun fahimci juna da goyawa juna baya, lamarin da ya kasance abin koyi wajen kafa sabuwar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa.

Xi ya sanar da cewa, za a daga huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wadanda suka kulla huldar diflomasiyya da Sin zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da kuma mai da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a matsayin dangantakar gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a dukkan fannoni cikin sabon zamani.

Fannonin sun hada da musayar al’adu, da bunkasa cinikayya, da hadin gwiwar tsarin samar da kayayyaki, da bunkasa harkokin sadarwa, da inganta harkokin kiwon lafiya, da raya aikin gona da tallafawa al’umma, da karfafa mu’amala a tsakanin jama’a, da kare muhalli, da kuma inganta ayyukan kiyaye tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments