A Aljeriya, yau Asabar ne ake bude rejistar zaben shugaban kasa da za’a gudanar a ranar 7 ga watan Satumba 2024.
‘Yan takara na da kwanaki 40 domin ajiye takardunsu domin neman tsayawa a zaben.
Shugaba Abdelmadjid Tebboune dai bai ce uffan ba game da makomarsa, amma gamayyarwasu jam’iyyu na yin kira da ya sake tsayawa takara a karo na biyu.
A makon da ya gabata an rawaito SHugaba Tebboune na shan alwashi gina kasar demokuradiyya mai karfi wanda masana ke kallo a matsayin sha’awar sake tsayawa takara.
Bayan jam’iyyun da suka hada da El Bina, FLN, RND da Front El-Mostaqbal da suke mara masa baya, akwai wasu jam’iyyu biyar da suka tsaida dan takara adawa a karkashin jam’iyyar UCP, inda Lauya Zoubida Assoul, zatayi musu takara.
A ranar 14 ga watan Agusta ne aka tsara fara yakin neman zabe a kasar.