Shugaban kasar Aljeriya,Abdelmadjid Tebboune, ya sake lashe zaben shugabancin kasar da gagarimin rinjaye.
An sake zaben ne a wa’adi na biyu da kashi 94.65% na kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar a jiya Asabar.
Daga cikin jimillar kuri’u miliyan 5.6, an zami Abdulmajid Tebboune da kuri’u miliyan 5.320 in ji, shugaban hukumar zaben kasar Mohamed Charfi.
Shugaban hukumar zaben ya sanar a ranar Asabar cewa an samu fitowar masu kada kuri’a da 48.03% “, idan aka kwatanta da 2019 da aka samu kasha (39.83%).
A waccan zaben, shugaban kasar ya lashe zaben ne da kashi 58% na kuri’un da aka kada.