Adadin Mutanen Da Suka Yi Shahada A Kasar Lebanon Sun Kai 2,968 Tare Da Jikkatan Wasu 13,319

Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren ta’addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan kasar Lebanon ya karu zuwa mutane 2,968 tare da jikkatan wasu 13,319

Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren ta’addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan kasar Lebanon ya karu zuwa mutane 2,968 tare da jikkatan wasu 13,319

Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa: Adadin wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan kasar ya haura zuwa shahidai 2,968, yayin da wadanda suka jikkata suka kai 13,319, inda ta bayyana cewa adadin wadanda suka mutu a ranar Juma’a suka kai shahidai 71 tare da jikkatan wasu 169 na daban.

Majiyoyin Lebanon sun tabbatar da cewa: Akalla mutane biyu ne suka yi shahada a wani farmaki da sojojin mamaya suka kaddamar a garin Mashghara, sannan ana ci gaba da neman mutanen da suka bata a garin.

Majiyoyin sun kara da cewa: Sojojin mamayar sun kuma kaddamar da farmaki kan wani gida a garin Hazrata da ke gabashin gundumar Zahle, inda suka kara da cewa jiragen saman yakin ‘yan mamaya sun kai farmaki a kan iyakar Hermel da Siriya, tare da yin luguden wuta kan yankin da ke kusa da garin Akrum, da kuma a kan iyakar Akkar bakarare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments